AREWA24 Za Ta Hau DStv Da GOtv A Oktoba

Transcript

AREWA24 Za Ta Hau DStv Da GOtv A Oktoba
AREWA24 Za Ta Hau DStv Da GOtv A Oktoba
Lagos, Nigeria; 17 October 2016: MultiChoice Nigeria zata dora AREWA24, a rukunin
tashoshinta domin fadada samar da tashoshi na kyauta (FTA) akan DStv da GOtv. Muna
gabatar da tashar farko ta tauraron Dan-Adam mai yada shirye-shiryenta awa 24 a harshen
Hausa kyauta ranar 20 October akan DStv channel 261 da kuma GOtv channel 101.
AREWA24 tasha ce ta nishadantarwa da harshen Hausa da take nuni ga rayuwar arewacin
Najeriya, al’adu, kirkire-kirkire da fito da albarkatun arewacin Najeriya ga masu Magana da
harshen Hausa a duk fadin Najeriya, Afirka, Gabas ta Tsakita da duk fadin duniya.
A sama da shekaru biyu kacal, tashar tana alfaharin zama wacce tafi samar da ingantattun
shirye-shirye da harshen Hausa domin al’umma masu magana da harshen Hausa.
Dangane da karin samun AREWA24 akan tashoshinmu na kyauta, John Uggbe Babban
Manajan MultiChoice Najeriya yace “Zamu bawa masu kallonmu kayatattun shirye-shirye su
zaba daga AREWA24”. Ya kara da cewa “Watannin da suka wuce, mun kara bunkasa
tashoshinmu na kyauta (FTA) da suka hada da tashoshin da masu kallonmu suka same su
masu ilimantarwa, da suke nuna dukkannin fannonin nishadantarwa. Kuma mun aminta da
cewa samar da Arewa 24 a rukunin tashoshinmu, karin arziki ne na samarwa masu kallonmu
shirye-shiryen gida a duk fadin Afirka”.
Da yake kara tsokaci akan hawa DStv da GOtv, Jacob Arback, Shugaban AREWA24 yace,
“Lokacin da muka kaddamar da AREWA24 sama da shekaru biyu da suka wuce, fatan mu
shine mu saduwa da miliyoyin ‘yan Arewa ta hanyar yaren Hausa da suke amfani da shi. Ina
da tabbacin cewa hadin gwiwar mu da MultiChoice wani karin mataki ne na cimma wannan
buri. Nasarar AREWA24 tana da alaka da shirye-shiryen da muke da su wadanda suka yi dai
dai da al’ada. Shirye-shiryenmu domin iyali ne da suke habaka al’ada ta hanyar labaru da
nishadantarwa.”
AREWA24 ita ce tashar kyauta FTA da zata hau DStv da GOtv. Sauran tashoshin kyauta sun
hada da; NTA I, Channels TV, Africa Independent Television (AIT), SilverBird Television, TVC,
Lagos Television, ONTV MAX, Wazobia TV, Trybe TV and Galaxy TV.
Game Da Arewa24: AREWA24 (arewa24.com) gidan talabijin din Arewacin Najeriya ne na farko a
tauraron Dan-Adam mai yada shirye-shiryensa 24/7 kyauta, wanda ke gabatar da shirye-shiryensa
akan rayuwar Arewacin Najeriya, al;adu, matasa, kasuwanci da nishadantar da iyali. AREWA24 ta
dukufa wajen habakawa da kuma cike gibin da masu magana da harshen Hausa suka rasa na shiryeshiryen Hausa a duk fadin duniya, wadanda da yawansu sukan kama tashar AREWA24 ta hanyar
yanar gizo domin ganin al’adarsu da kuma ta sauran mutanen duniya. Ana dora shirye-shiryen
AREWA24 na kashin kanta kowane sati a youtube.com/AREWA24channel, kuma tashar tana karuwa
da
masu
kallonta
ko
da
yaushe
a
AREWA24.com,
Facebook.com/AREWA24,
Instagram.com/AREWA24channel, da twitter.com/AREWA24channel. AREWA24 tana kan EUTELSAT
16A, horizontal polarization, frequency 10804, symbol rate 30000 da kuma tauraron Dan-Adam na
ACTV. Abokan huldar AREWA24 sun hada da Jordan Media City, Eutelsat da Globecast. Ana rarraba
shirye-shiryen AREWA24 na kashin kanta a duk fadin Arewacin Najeriya tare da hadin gwiwar
hukumar talabijin ta Najeriya (NTA). Tashoshin da suka fara gudanar da wannan hadakar ta NTAAREWA24 sun hada da NTA-Abuja, NTABauchi, NTA-Kaduna, NTA-Kano, NTA-Maiduguri da NTASokoto, kuma zamu ci gaba da kutsawa cikin sauran tashoshin NTA a Arewacin Najeriya gaba dayan
wannan shekarar.
Don samun karin bayani sai a ziyarci shafin www.dstv.com ko kuma www.gotvafrica.com
###