Zai Yiwu A Sake Rayuwa
Transcript
Zai Yiwu A Sake Rayuwa
SATUM BA – O KTO BA 2 0 1 5 34567 Zai Yiwu A Sake Rayuwa BAYAN MUTUWA? 34567 Vol. 136, Na 17 ˙ Bugun Kowace Fitowa: 52,946,000 A HARSUNA 243 SATUMBA–OKTOBA 2015 Monthly and supplemental bimonthly editions HAUSA WANNAN MUJALLAR, Hasumiyar Tsaro, ana buga ta ne don girmama Jehobah Allah, Mamallakin sama da asa. Tana arfafa mutane cewa Mulkin Allah zai kawar da dukan mugunta kuma ya mai da duniya aljanna ba da daewa ba. Tana sa a ba da gaskiya ga Yesu Kristi, wanda ya mutu domin mu sami rai madawwami kuma wanda a yanzu shi ne Sarkin Mulkin Allah. An soma buga wannan mujallar babu fashi tun daga shekara ta 1879. Wannan mujallar ba ta siyasa ba ce. Littafi Mai Tsarki ne madogaranta. ABIN DA KE SHAFIN FARKO Za ka so arin bayani ko kuwa nazarin Littafi Mai Tsarki a gidanka kyauta? A FITOWAR NAN Zai Yiwu A Sake Rayuwa—Bayan Mutuwa? SHAFUFFUKA NA 3-8 Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa? 3 Matattu Suna da Bege Kuwa? 5 Me Zai Iya Tabbatar Maka Cewa Matattu Za Su Sake Rayuwa? 7 Ka Sani? 9 Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane Ka shiga dandalin www.jw.org/ha ko kuma ka aika sao zuwa ga aya daga cikin waannan adireshin da ke asa. Na NIJERIYA: Jehovah’s Witnesses P.M.B. 1090 Benin City 300001 Edo State ¯ Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Da 10 Za Mu Iya Faranta wa Allah Rai Kuwa? 12 Ka Sani? 15 Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki 16 Na BENIN: ´ ´ Les Temoins de Jehovah B.P. 312 AB-Calavi Za ka sami cikakken jerin adireshinmu a www.jw.org/ha/hanyar-tuntuba. ˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙˙ Wannan mujallar ba ta sayarwa ba ce. Sashe ce ta aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki a dukan duniya wadda ake tallafa wa da gudummawar da aka ba da da son rai. An auko nassosin da aka yi amfani da su a nan ne daga Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauae. A duk inda kuka ga an rubuta LMT, ana nufin an yi aulin wata fassarar Littafi Mai Tsarki ne. Idan kuma kuka ga NW, ana nufin an yi aulin fassarar New World Translation. The Watchtower (ISSN 0043-1087) is published semimonthly by Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc.; L. Weaver, Jr., President; G. F. Simonis, Secretary-Treasurer; 25 Columbia Heights, Brooklyn, NY 11201-2483, and by Watch Tower Bible and Tract Society of Canada, PO Box 4100, Georgetown, ON L7G 4Y4. Periodicals Postage Paid at Brooklyn, NY, and at additional mailing offices. POSTMASTER: Send address changes to Watchtower, 1000 Red Mills Road, Wallkill, NY 12589-3299. 5 2015 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. Printed in Nigeria. s ZA KA SAMI ARIN BAYANI A INTANE AMSOSHI GA ARIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI SATUM BA – O KTO BA 2 0 1 5 34567 Me Zai Taimaka Mini In Daina Tsoron Mutuwa? Zai Yiwu A Sake Rayuwa BAYAN MUTUWA? KA SAUKO DA WANNAN MUJALLAR A DANDALINMU r 5 sablin/123RF Stock Photo (Ka danna KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI ˛ AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI) ABIN DA KE SHAFIN FARKO Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa? “Na auka cewa idan mutum ya mutu yana iya zuwa wurare uku, wato sama ko gidan wuta ko kuma purgatori. Na san cewa ban cancanci zuwa sama ba kuma ban yi abubuwan da suka isa in shiga gidan wuta ba. Ban san ainihi abin da purgatori yake nufi ba. Ban taa ganin kalmar a cikin Littafi Mai Tsarki ba, age ne kawai.”—In ji Lionel. “An koya mini cewa dukan waanda suka mutu suna zuwa sama amma ban gamsu da hakan ba. Na ga kamar mutuwa ce arshen kome, wato babu wani bege ga matattu.” —In ji Fernando. Ka taa yin irin wannan tambayar: ‘Mene ne ke faruwa da mutane sa’ad da suka mutu? Matattu suna shan azaba a wani wuri ne? Za mu sake ganinsu kuwa? Ta yaya za mu tabbata da hakan?’ Don Allah ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya faa game da wannan batun. Bari mu fara bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa. Bayan haka, sai mu tattauna begen da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai. SATUMBA–OKTOBA 2015 3 Mene ne yanayin matattu? ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Masu-rai sun san za TASHIN MATATTU TAKWAS DA AKA AMBATA A LITTAFI MAI TSARKI1 Yaron wata gwauruwa Annabi Iliya ya ta da yaron wata gwauruwa da ke Zarefat a arewacin Isra’ila.—1 Sarakuna 17:17-24. an wata Ba-shunammiya Elisha magajin annabi Iliya ya ta da wani yaro a garin Shunem kuma ya mia shi ga iyayensa.—2 Sarakuna 4: 32-37. Wani mutum a makabarta An binne gawan wani da bai dae da mutuwa ba a inda aka binne annabi Elisha. Mutumin ya tashi sa’ad da gawarsa ta taa asusuwan annabi Elisha. —2 Sarakuna 13:20, 21. an wata gwauruwa a auyen Nayin Yesu ya dakatar da wata jana’izar da ake yi a garin Nayin kuma ya ta da wannan matashin, ya mai da shi ga mahaifiyarsa da ke makoki.—Luka 7: 11-15. ’Yar Yariyus Wani ma’aikacin majami’a mai suna Yariyus ya kira Yesu don ya warkar da ’yarsa da ke rashin lafiya. Yesu ya ta da ita jim kaan bayan ta rasu.—Luka 8:41, 42, 49-56. Li’azaru, abokin Yesu Yesu ya ta da Li’azaru bayan kwanaki huu da mutuwa kuma mutane da yawa sun shaida wannan aukuwar.—Yohanna 11:38-44. Wata mai suna Dokas Manzo Bitrus ya ta da wannan matar wadda aka san ta da ayyukan nagarta.—Ayyukan Manzanni 9:36-42. Aftikos Manzo Bulus ya ta da wani matashi mai suna Aftikos da ya fao daga tagar wata bene.—Ayyukan Manzanni 20:7-12. 1 Tashin matattu mafi muhimmanci shi ne na Yesu Kristi kuma ya bambanta da waannan takwas da muka tattauna. Abin da za a tattauna a talifi na gaba ke nan. 4 HASUMIYAR TSARO su mutu: amma matattu ba su san kome ba, ba su kuwa da sauran lada; gama ba a ara tuna da su ba. Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da arfinka; gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.”1—Mai-Wa’azi 9:5, 10. Kabari wuri ne da ake saka mutane sa’ad da suka mutu, ba wuri ne na zahiri ba domin mutanen da suke wurin ba su san kome ba kuma ba sa aiki. Wane ra’ayi ne Ayuba mai aminci yake da shi game da Kabari? Ya yi asarar dukiyarsa da ’ya’yansa a rana aya kuma Shaian ya addabe shi da gyambuna. Ya roi Allah: “Da fa za ka yarda ka oye ni cikin Lahira [‘Kabari,’ New World Translation].” (Ayuba 1:13-19; 2:7; 14:13) Hakika, Ayuba bai auka cewa Kabari gidan wuta ba ne inda wahalar da yake sha za ta daa aruwa ba. Maimakon haka, ya san cewa wurin hutu ne. Akwai wata hanya kuma da za mu iya koya game da yanayin matattu. Littafi Mai Tsarki yana auke da labaran mutane takwas da suka tashi daga mutuwa da za mu iya yin bincike a kansu.—Ka duba akwatin nan “Tashin Matattu Takwas da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki.” Babu ko aya cikin mutane takwas da aka ambata da ya je sama ko kuma gidan wuta. Da a ce waanda aka tashe su sun je irin waannan wuraren, kana ganin da ba su ba mutane labari ba? Kuma da ba a rubuta hakan a cikin Littafi Mai Tsarki don mutane su karanta ba? Ba a rubuta kome game da hakan a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Babu shakka, waannan mutane takwas ba su ce kome ba game da wannan batun. Me ya sa? Domin a lokacin da suka mutu ba su san kome ba, kamar sun yi barci ne mai zurfi. Hakika a wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki yakan kwatanta mutuwa da barci. Alal misali, amintattun mutane kamar Dauda da Istafanus sun “yi barci,” wato sun mutu. —Ayyukan Manzanni 7:60; 13:36. To, wane bege ne matattu suke da shi? Za su iya farka daga wannan barci kuwa? 1 An yi amfani da kalmar nan “Kabari” a wuraren da kalmomin Ibranancin nan “Sheol” da kuma na Helenanci “Hades” suka bayyana. Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “jahannama” amma Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa ana one mutane a wuta ba. Matattu Suna da Bege Kuwa? Shin matattu za su sake rayuwa kuwa? ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Sa’a tana zuwa, inda dukan waanda suna cikin kabarbaru za su ji muryar [Yesu], su fito kuma.’—Yohanna 5:28, 29. Yesu ya yi annabci a kan lokacin da za a ta da dukan mutanen da suke cikin Kabari sa’ad da ya soma sarauta. Fernando da aka ambata a talifi na farko ya ce: “Na yi mamaki sosai a lokacin da na fara karanta littafin Yohanna 5:28, 29. Hakan ya sa na kasance da bege sosai kuma na soma yin tunani game da nan gaba da gaba gai.” ¯ Ayuba mai aminci ya sa rai cewa A zamanin da, Allah zai ta da shi idan ya mutu. Ayuba ya yi wannan Tashin Li’azaru daga mutuwa ya sa mun kasance da bege tambayar: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” Sai ya amsa da gaba gai: “Dukan kwanakin yaina [lokacin da nake kabari] sai in jira, har a kare ni in huta. Za ka yi kira, ni ma in amsa maka.” —Ayuba 14:14, 15. Tashin matattu ba sabon abu ba ne ga Martha, ’yar’uwar Li’azaru. Bayan Li’azaru ya mutu, Yesu ya ce mata: “an’uwanki zai tashi kuma.” Martha ta ce masa: “Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta arshe.” Sai Yesu ya ce mata: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu.” (Yohanna 11:23-25) Bayan haka, sai Yesu ya ta da Li’azaru daga mutuwa! Wannan labarin soma tai ne na abin da zai faru a nan gaba. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance idan an ta da matattu a dukan duniya! Shin za a ta da wasu zuwa sama ne? ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Kalmar Allah ta nuna cewa tashin Yesu da aka yi daga mutuwa ya bambanta da guda takwas da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. An ta da waannan mutane takwas a duniya. Amma ga abin da nassi ya ce game da na Yesu: “Yesu Kristi; shi wanda ke ga hannun dama na Allah, ya rigaya ya hau sama.” (1 Bitrus 3:21, 22) Ban da Yesu, shin da akwai wasu kuma da za a ta da zuwa sama? Yesu ya ce wa manzanninsa: “In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can.”—Yohanna 14:3, Littafi Mai Tsarki. Kristi ya je sama kuma ya yi shirye-shirye don zuwan wasu cikin almajiransa. Adadin mutane 144,000 ne za su je sama. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3) Amma mene ne waannan mabiyan Yesu za su yi a sama? SATUMBA–OKTOBA 2015 5 Dukan mutanen da suke bauta wa Allah za su yi rayuwa har abada cikin oshin lafiya da kuma farin ciki Za su yi aiki tuuru! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maialbarka kuma mai-tsarki ne shi wanda yake da rabonsa cikin tashi na fari: mutuwa ta biyu ba ta da iko bisansu; amma za su zama firistoci na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.” (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Mutanen da za a ta da zuwa sama za su zama sarakuna da kuma firistoci tare da Kristi kuma za su yi sarauta bisa duniya. Su waye za a tayar daga baya? ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: An rubuta wannan furucin manzo Bulus cikin Nassosi: “Ina da bege ga Allah, abin da waannan da kansu kuma suna sauraronsa, za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.”—Ayyukan Manzanni 24:15. Su waye ne “masu adalci” da Bulus ya ambata? Ga wani misali. Daniyel mutumi ne mai adalci kuma sa’ad da ya kusan mutuwa, an gaya masa cewa: Za “ka huta, a arshen kwanaki za ka tashi ka kari naka rabo.” (Daniyel 12:13, LMT) A ina ne za a ta da ¯ aDaniyel daga mutuwa? “Masu-adalci za su gaji san, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Kuma Yesu ya yi wannan annabcin: “Masu-albarka ¯ duniya.” (Matne masu-tawali’u: gama su za su gaji ta 5:5) Za a ta da Daniyel da kuma wasu amintattun maza da mata don su sake rayuwa a duniya har abada. Su waye ne “marasa adalci” da Bulus ya ambata? Su biliyoyin mutane ne da suka mutu, da yawa cikinsu ba su sami zarafin fahimta da kuma aikata gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. Bayan sun tashi daga mutuwa, za su sami zarafin sanin Jehobah1 da kuma Yesu. (Yohanna 17:3) Dukan mutanen da suka yanke shawarar bauta wa Allah za su yi tsawon rayuwa kamar Jehobah, wato za su rayu har abada. Yaya rayuwa za ta kasance a duniya? ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Allah “zai share du- Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa biliyoyin mutanen da suka mutu za su sake rayuwa kan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ara kasancewa ba; ba kuwa za a ara yin bain ciki, ko kuka, ko azaba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu.”—Ishaya 65:21. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da kake cikin irin wannan yanayin tare da mutanen da aka tayar daga mutuwa! Amma akwai wata tambaya da ba a amsa ba tukun, Ta yaya za ka kasance da tabbaci cewa za a ta da matattu? 1 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah. 6 HASUMIYAR TSARO Me Zai Iya Tabbatar Maka Cewa MATATTU ZA SU SAKE RAYUWA? Shin ata lokaci ne yin tunani cewa matattu za su sake rayuwa? Manzo Bulus bai kasance da wannan ra’ayin ba. Allah ya hure shi ya ce: “Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi. Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waanda suka yi barci.” (1 Korintiyawa 15:19, 20, Littafi Mai Tsarki) Bulus yana da tabbaci sosai cewa za a ta da matattu. Tashin Yesu daga mutuwa ne ya ba da wannan tabbacin.1 (Ayyukan Manzanni 17:31) Shi ya sa Bulus ya kira Yesu “nunan fari,” domin shi ne mutumi na farko da ya tashi daga mutuwa da ba zai sake mutuwa ba har abada. Idan Yesu ne na fari, to babu shakka, akwai wasu da za su biyo bayansa. Ga wani dalili kuma da ya sa za mu iya gaskatawa da begen tashin matattu. Jehobah Allah yana fain gaskiya a koyaushe. “Allah . . . ba ya iya yin arya.” (Titus 1:2) Jehobah bai taa yin arya ba kuma ba zai taa yin hakan ba. Shin zai yiwu ya yi mana alkawarin tashin matattu, ya nuna cewa yana da ikon yin hakan, sa’an nan daga baya ya fasa cika alkawarinsa? Babu shakka, hakan ba zai yiwu ba! Me ya sa Jehobah ya yi alkawari cewa zai ta da matattu? Domin yana aunarmu. Ayuba ya yi wannan tambayar: ‘Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa? . . . Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.’ (Ayuba 14:14, 15) Ayuba ya tabbata cewa Ubansa na sama zai yi marmarin tayar da shi. Shin Allah ya canja ne? Jehobah ¯ ya ce: “Ni Ubangiji ba mai-sakewa ba ne.” (Malakai 3:6) Har ila, Allah yana okin tayar da waanda suka mutu kuma su kasance da oshin lafiya da farin ciki. Abin da mahaifi mai auna zai so ya faru Ayuba ya gaya wa Allah: “Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.”—Ayuba 14:14, 15 1 Don tabbaci cewa an ta da Yesu daga mutuwa, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2014, shafi na 6, sakin layi na 11-14. SATUMBA–OKTOBA 2015 7 Mutuwa maiyiya ce, amma Allah zai kawar da ita ke nan bayan ansa da ya mutu. Bambancin shi ne Allah yana da ikon yin abin da ya nufa.—Zabura 135:6. Jehobah zai ba ansa iko ya sa masu makoki su yi matuar farin ciki. Mene ne ra’ayin Yesu game da tashin matattu? Yesu ya yi “kuka” kafin ya tayar da Li’azaru don ya ga irin bain ciki da ’yan’uwansa da kuma abokansa suka yi. (Yohanna 11:35) A wani lokaci kuma, Yesu ya ga wata gwauruwa a auyen Nayin da anta tilo ya mutu. Yesu “ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, ‘Daina kuka.’ ” Nan da nan sai ya tayar da anta. (Luka 7:13, LMT) Saboda haka, Yesu ba ya jin dain ganin mutane suna makoki da kuma mutuwa. Zai yi murna sosai sa’ad da ya sa dukan mutanen da ke makoki a duniya baki aya farin ciki! An taa maka rasuwa kuwa? Za ka iya auka cewa ba za a iya kawar da mutuwa ba. Amma hakan ba gaskiya ba ne, Allah zai yi amfani da ansa don ya tayar da mutanen da suka rasu. Ka tuna cewa Allah yana so ka shaida lokacin da za a ta da matattu. Yana so ka kasance a wurin don ka marabci ’yan’uwanka da za a tayar daga mutuwa. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da mutuwa ta zama tsohon labari! Lionel da aka ambata azun ya ce: “Daga baya sai na koya cewa za a yi tashin matattu. Da farko, ban gaskata da hakan ba domin na yi shakkar mutumin da ya gaya mini. Amma da na bincika Littafi Mai Tsarki sai na ga cewa hakan gaskiya ne! Ina okin sake ganin kakana.” Za ka so ka sami arin bayani? Shaidun Jehobah za su yi farin cikin nuna maka a cikin naka Littafi Mai Tsarki cewa za a ta da matattu.1 ˇ 1 Ka duba babi na 7 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa. Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha. 8 HASUMIYAR TSARO KA SANI? Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, ¯ mene ne kalmar nan baba take nufi? ¯ HOTON BABA A ASIRIYA 5 The Metropolitan Museum of Art, Image source: Art Resource, NY ¯ A wasu lokuta, ana amfani da kalmar nan baba don a kwatan¯ ta namijin da aka yi masa dandae. A da, an yi wa wasu maza dandae don sun yi wani laifi ko bayan an ci su a yai ko kuma sa’ad da suka zama bayi. Ana amfani da mazan da aka yi musu dandae wajen gadin matan sarki ko kuma wani attajiri. Alal mi¯ sali, baba Hegai da Sha’ashgaz sun yi aiki ne a matsayin masu gadin matan Sarki Ahasurus ko kuma Xerxes na aya.—Esther 2:3, 14. ¯ Amma ba dukan waanda Littafi Mai Tsarki ya kira su baba ne aka yi musu dandae ba. Wasu masana sun ce kalmar tana da manufa da yawa, tana iya nufin wani babban ma’aikaci a fadar sarki. Wataila abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce da ¯ Ebed-melech, abokin aikin Irmiya baba kuma ya ce da wani Bahabashe wanda Filibus ya yi ma wa’azi ma hakan. Ebed-melech babban ma’aikacin sarki ne don yana da ’yancin zuwa wurin Sarki Zedekiya. (Irmiya 38:7, 8) Kuma an kwatanta Bahabashen a matsayin ma’ajin sarauniya da ya je “Urushalima . . . garin yin sujada.”—Ayyukan Manzanni 8:27. ˇ ¯ Me ya sa makiyaya a zamanin da suke ware tumaki daga awaki? 5 World Religions Photo Library/Alamy Sa’ad da Yesu yake kwatanta hukuncin da za a yi a nan gaba, ya ce: ‘Sa’ad da an Mutum ya zo cikin aukaka tasa . . . zai kuma ware mutane dabam-dabam, kamar yadda makiyayi ke ware tumaki da awaki.’ (Matta 25:31, 32, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa makiyaya suke ware tumaki daga awaki? Ana yawan yin kiwon awaki da tumaki tare da rana. Amma daddare, ana shinge su saboda namomin daji ko arayi ko kuma sanyi. (Farawa 30:32, 33; 31:38-40) Ana ware tumaki daga awaki domin kada awakin su ji wa tunkiya ko kuma ’ya’yansu rauni. Littafin nan All Things in the Bible ya ce: “Makiyaya suna kuma ware tumaki daga awaki sa’ad da suke tatse nono da yanke gashinsu da kuma sa’ad da suka haihu.” Saboda haka, kwatancin Yesu sananne ne ga masu sauraronsa da ke zama a wuraren da ake kiwo kamar a asar Is¯ ra’la ta da. ˇ SATUMBA–OKTOBA 2015 9 LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE Na yi rayuwar banza ¯ sosai a da STEPHEN MCDOWELL NE YA BA DA LABARIN SHEKARAR HAIHUWA 1952 ASAR HAIHUWA AMIRKA TARIHI MAI ZAFIN RAI ¯ RAYUWATA A DA: Na yi girma a birnin Los Angeles, Kalifoniya a asar Amirka kuma na zauna a unguwar da ke cike da ’yan iska da kuma masu shan miyagun wayoyi. Iyayena sun haifi yara shida kuma ni ne na biyu a cikinsu. Mahaifiyarmu ta rene mu a wani coci mai suna evangelical church. Amma sa’ad da nake tsakanin shekara sha uku zuwa sha tara, na soma yin rayuwar banza. A ranar Lahadi nakan yi waa a cocinmu. A wasu ranakun kuma sai in je fati, in sha miyagun wayoyi kuma in yi lalata. Ina yawan fushi da kuma zafin rai. Ina amfani da kowane abu don in ji ma mutane rauni. Abin da na koya a coci bai taimaka mini ba sam. Nakan ce, “Ramako na Ubangiji ne, kuma da ni zai cim ma hakan!” Sa’ad da nake makarantar sakandare a arshen shekara ta 1960, na shiga wani rukunin da ke yai don ’yancin alibai. Wani rukunin siyasa da ke yai don ’yancin masu farar hula da ake kira Black Panthers ne ya rinjaye ni yin hakan. A lokatai da yawa mukan ta da rigima har ma a rufe makarantar na an lokaci. Ban gamsu da zanga-zanga da nake yi ba, saboda haka, na soma aikata laifi don ina iyayyar mutane. Alal misali, akwai lokacin da muka kalli wani fim da ya nuna yadda ’yan Amirka suke wulaanta ’yan Afir¯ Da muka ji haushi, sai muka yi wa turawan da ke gidan siliman ka a da. ¯ dukan tsiya. Bayan haka, sai muka shiga unguwoyi muna neman tura¯ wan za mu yi wa duka. Da na kusan shekara ashirin, ni da annena biyu da kuma yayana mun ware sosai a aikata manyan laifuffuka. Saboda haka, muna yawan samun saani da hukuma. anina yana cikin wani sanannen rukuni mai ta da rikici, kuma ni ma ina bin su. Rayuwata sai daa muni take yi. YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Ina da abokin da iyayensa Shaidun Jehobah ne. Sun gayyace ni zuwa taronsu kuma na je. Wannan ne aro na farko da na ga cewa halin Shaidun Jehobah dabam ne. Na lura cewa kowa yana amfani da Littafi Mai Tsarki a taron kuma matasa ma suna yin jawabai! Na yi farin cikin sanin cewa sunan Allah Jehobah ne kuma na ji suna amfani da shi. (Zabura 83:18) Babu wata wariya a ikilisiyar duk da cewa mutanen daga kabilu dabam-dabam ne. Da farko na so halartan taron Shaidun Jehobah amma ban so yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su ba. Akwai wata rana da na je taron 10 HASUMIYAR TSARO Shaidun Jehobah da yamma, amma abokaina kuma sun je fati. A wurin suka kashe wani matashi don ya i ya ba su kwat insa. Washegari, sai suka yi ta cika baki game da kisan da suka yi. Sa’ad da aka kai su kotu, ba su auka cewa sun aikata babban laifi ba. A sakamakon haka, an yi wa yawancinsu aurin rai da rai. Na yi farin ciki cewa ban bi su a wannan ranar ba. A lokacin ne na tsai da shawarar canja rayuwata da kuma soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Da yake na saba gani ana nuna wariyar kabila, hakan ya sa ni mamaki sosai sa’ad da na lura cewa halin Shaidun Jehobah dabam ne. Alal misali, akwai lokacin da wani bature ya tafi asarsu kuma ya bar yaransa a hannun wani bain fata don ya kula da su. Ban da wannan ma, na ga wani iyalin turawa sun ce wa wani matashi bain fata da ke neman gida ya zo ya zauna da su. Hakan ya sa na gaskata cewa Shaidun Jehobah ne suka yi daidai da kwatancin Yesu a Na yi oari sosai in canja salon rayuwata don in yi zaman lafiya da mutane kuma na tabbata cewa wannan ita ce hanyar da ta dace littafin Yohanna 13:35 cewa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da auna ga junanku.” Wannan ya sa na yarda cewa na sami addini na gaskiya. Nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi ya sa na fahimta cewa ya kamata in canja ra’ayina. Na yi oari sosai in canja salon rayuwata don in yi zaman lafiya da mutane kuma na tabbata cewa wannan ita ce hanyar da ta dace. (Romawa 12:2) Da sannu-sannu na samu ci gaba kuma a watan Janairu na shekara ta 1974, na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah. Amma har bayan na yi baftisma, na ci gaba da yin oari don in rage zafin rai. Alal misali, na taa bin wani arawo da ya saci rediyo a motata sa’ad da nake wa’azi. Da ya ga cewa na yi kusa da shi, sai ya yar da rediyon ya gudu. Sa’ad da na gaya wa waan- da muke wa’azi tare da su abin da ya faru, sai wani dattijo a cikinsu ya tambaye ni, “Stephen, da a ce ka kama shi me za ka yi masa?” Tambayar ta sa in san cewa ina bukatar in yi oari don in zauna lafiya da mutane. A watan Oktoba ta 1974, na soma hidima ta cikakken lokaci, ina yin sa’o’i ari a kowane wata don koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Daga baya, an gayyace ni yin hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Brooklyn, a Amirka. A shekara ta 1978, na koma birnin Los Angeles don in kula da mahaifiyata da ke rashin lafiya. Bayan shekara biyu, sai na auri wata mai suna Aarhonda. Ta taimaka mini sosai wajen kula da mahaifiyata har zuwa lokacin da ta rasu. Bayan haka, sai aka gayyace mu zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead kuma da muka sauke karatu, an tura mu zuwa asar Panama, inda muka yi hidima a matsayin masu wa’azi a asashen waje. Tun da na yi baftisma, na fuskanci wasu yanayoyin da za su iya sa in yi faa. Amma na yi oarin guje wa mutanen da suke so su sa ni fushi ko kuma ina yin amfani da wata dabara don kada abin ya jawo faa. Matata da mutane da yawa sun yaba mini don yadda na bi da waannan yanayoyin kuma yadda na bi da yanayin ya ba ni mamaki sosai. Na san cewa ba da ikona nake yin waannan canje-canjen ba. Maimakon haka, na tabbata cewa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka mini in yi hakan.—Ibraniyawa 4:12. YADDA NA AMFANA: Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in yi rayuwa mai ma’ana kuma in zauna lafiya ¯ da mutane. Na daina dukan mutane yanzu, amma ina taimaka musu su san Allah. Har ma na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wani da muke yawan faa da shi sa’ad da muke makaranta. Bayan da ya yi baftisma, mun soma zama a dai aya da shi. Har wa yau, mu abokai ne sosai. Tun daga lokacin har zuwa yau, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane sama da 80 kuma sun zama Shaidun Jehobah. Ina godiya ga Jehobah sosai don ya taimaka mini in yi rayuwa mai ma’ana da farin ciki a tsakanin ’yan’uwana Shaidun Jehobah. ˇ SATUMBA–OKTOBA 2015 11 ‘[Allah] ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya bakinta masa rai warai.’—2 Bitrus 2:7 Za Mu Iya Faranta wa Allah Rai Kuwa? Ka taa karanta labarin wasu da aka yaba musu sosai a Littafi Mai Tsarki kuma ka ce wa kanka, ‘Ba zan iya zama kamar waannan mutanen ba!’ Kana iya cewa, ‘Ni ba kamili da kuma mai adalci ba ne kuma ba na yin abin da ya dace a koyaushe.’ 12 HASUMIYAR TSARO Littafi Mai Tsarki ya ce Ayuba “kamili ne maiadalci” kuma. (Ayuba 1:1) Ya kuma ce Lutu “maiadalci” ne. (2 Bitrus 2:8) Kuma ya ce Dauda ya “yi abin da ke daidai” a idanun Allah. (1 Sarakuna 14:8) Amma bari mu tattauna wasu abubuwa game da rayuwar waannan mutanen. Za mu ga cewa sun yi (1) kura-kurai, (2) za mu iya koyan darussa daga wurinsu, kuma (3) zai yiwu ’yan Adam ajizai su faranta wa Allah rai. SUN YI KURA-KURAI Ayuba ya fuskanci matsaloli dabam-dabam kuma ya ji kamar ana masa rashin adalci. Saboda haka, ya kasance da ra’ayi marar kyau domin ya yi zato cewa Allah bai damu ko shi mai adalci ne ko marar adalci ba. (Ayuba 9:20-22) Ayuba ya tabbata sosai cewa shi mai adalci ne har ya soma ji kamar ya fi Allah adalci.—Ayuba 32:1, 2; 35:1, 2. Lutu ya yi jinkirin yanke shawarar da ta dace. Lalatar mutanen Saduma da Gwamarata ta sa shi Dauda ‘ya bi [Allah] da dukan zuciyarsa, domin ya yi abin da ke daidai a idanun [Allah] kaai.’ —1 Sarakuna 14:8 Ayuba “kamili ne mai-adalci” kuma. —Ayuba 1:1 bain ciki sosai har “ya azabtar da ransa maiadalci” domin ayyukansu. (2 Bitrus 2:8) Allah ya gaya wa Lutu cewa yana so ya halaka biranen kuma ya ba shi da iyalinsa damar tsere wa halakar. Shin Lutu ya bar birnin da gaggawa kuwa? A’a. Ya yi jinkiri a wannan lokacin. Har sai da mala’ikan da aka tura wajensu ya kama hannunsu kuma ya fitar da su daga birnin.—Farawa 19:15, 16. Dauda ya taa kasancewa da rashin kamun kai kuma hakan ya sa ya yi zina da matar wani. Abin bain ciki, ya kashe mijin matar garin neman ya rufe wa kansa asiri. (2 Sama’ila, sura ta 11) Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “bai ji dain mugun abin da Dauda ya yi ba.”—2 Sama’ila 11:27. Ayuba da Lutu da kuma Dauda sun yi kurakurai, wasu masu tsanani ne sosai. Amma za mu tattauna yadda suka nuna cewa suna so su bauta wa Allah da aminci da kuma zuciya aya. Sun kasance a shirye su nuna cewa laifin da suka yi bai dace ba kuma su yi gyara a inda suke bukatar yin Allah “ya san abin da aka yi mu da shi, yakan tuna, da ura aka yi mu.”—Zabura 103:14 hakan. Shi ya sa Allah ya amince da su kuma Littafi Mai Tsarki ya ce su amintattu ne. WANE DARASI NE ZA MU IYA KOYA? Babu yadda za mu guji yin kura-kurai domin mu ajizai ne. (Romawa 3:23) Amma idan hakan ya faru, muna bukatar mu nuna cewa muna dana-sani kuma muna so mu yi gyara. Ta yaya Ayuba da Lutu da kuma Dauda suka yi gyara? Ayuba mutumi ne mai aminci. Sa’ad da Allah ya yi wa Ayuba gyara, ya amince da hakan SATUMBA–OKTOBA 2015 13 Zuciya aya tana nufin zuciyar da ke aunar Allah kuma ke son yin nufinsa kuma ya yi da-na-sani don abubuwan da ya faa. (Ayuba 42:6) Allah ya tsani lalatar da mutanen Saduma da Gwamarata suke yi, Lutu ma haka. Matsalarsa kawai ita ce jinkirin da ya yi. Daga baya ya fita daga birnin kuma ba a halaka shi ba. Lutu ya yi biyayya ta wajen in juya baya don ya kalli abubuwan da ya bari. Ko da yake Dauda ya yi laifi mai tsanani ta wajen taka dokar Allah, ya tuba kuma ya nemi gafara. Hakan ya nuna cewa yana aunar Allah sosai.—Zabura ta 51. Yadda Allah ya bi da waannan mutanen ya yi daidai da ra’ayinsa game da ’yan Adam ajizai. Allah “ya san abin da aka yi mu da shi, yakan tuna, da ura aka yi mu.” (Zabura 103:14, Littafi Mai Tsarki) Idan Allah ya san cewa ba zai yiwu mu guji yin kura-kurai ba, to, wane ra’ayi ne yake so mu kasance da shi? TA YAYA MUTANE AJIZAI ZA SU IYA FARANTA WA ALLAH RAI? Shawarar da Dauda ya ba ansa Sulemanu ta nuna abin da ya kamata mu yi don mu faranta wa Allah rai. Dauda ya ce: “Kai kuwa ana Sulemanu, sai ka san Allah na [ubanka], ka bauta masa da zuciya aya.” (1 Labarbaru 28:9, LMT) Mene ne furucin nan zuciya aya yake nufi? Yana nufin zuciyar da ke aunar Allah kuma ke son yin nufinsa. Ba ya nufin kamiltacciyar zuciya, amma zuciyar da ke marmarin bauta wa Allah cikin aminci kuma take a shirye ta yi gyare-gyare. Allah ya kira Ayuba “kamili,” Lutu “mai-adalci” kuma Dauda mutumin da ke yin “abin da ke daidai” a idanun Allah a koyaushe domin sun aunace shi kuma sun yi okin yin biyayya gare shi. Ko da yake sun yi kura-kurai, amma sun yi abubuwan da suka faranta wa Allah rai. Saboda haka, idan mun yi tunanin banza ko mun yi wani abu da daga baya muka san cewa bai dace ba, ya kamata mu yi la’akari da misalan da muka tattauna a wannan talifin. Allah ya san cewa mu ajizai ne. Amma yana so mu aunace shi kuma mu oarta don mu yi masa biyayya. Idan muna bauta wa Allah da zuciya aya, za mu iya kasance da gaba gai cewa mu ma za mu iya faranta masa rai. ˇ 14 HASUMIYAR TSARO KA SANI? Wane ’yanci ne manzo Bulus ya samu domin ya zama an asar Roma? BULUS YA CE: “A AUKAKA ARATA GABAN KAISAR!” Zama an asar Roma yana ba mutum ’yanci da kuma zarafi da yawa a kowane wuri da ya shiga a cikin daular. Duk mutumin da ke da ’yancin zama an asar Roma yana arashin dokar asar ne ba na biranen da ke asar ba. Sa’ad da aka tuhume shi da aikata laifi, za a iya shari’anta shi a birnin, amma yana da ’yancin aukaka ara zuwa babban kotun asar. Idan kuma an yanke masa hukuncin kisa, zai iya aukaka arar zuwa wajen sarkin asar. Irin wannan ’yancin ne ya sa wani an siyasa a arni na farko kafin haihuwar Yesu, mai suna Cicero ya ce: “Kama an asar Roma laifi ne; yi masa duka mugunta ne; kashe shi kuma aya ne da wani ya kashe mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko kuma wani danginsa.” Manzo Bulus ya yi wa’azi sosai a Daular Roma. Ya yi amfani da ’yancinsa na an asar Roma a hanyoyi uku: (1) Ya gaya wa alalan Filibi cewa sun taka ’yancinsa ta wajen yi masa dua. (2) Sa’ad da yake Urushalima, ya fai cewa shi an asar Roma ne domin kada a doke shi. (3) Ya aukaka ararsa zuwa gaban Kaisar, wanda shi ne sarkin Roma, domin ya yanke hukuncin da kansa.—Ayyukan Manzanni 16:37-39; 22:25-28; 25:10-12. ˇ ¯ Ta yaya ake biyan makiyaya a zamanin da? ALLON DUTSEN DA AKA RUBUTA KWANGILAR TUMAKI DA KUMA AWAKI DA AKA SAYA, A WAJEN SHEKARA TA 2050 K.Z.Y. Yakubu uban iyali ya yi kiwon garken kawunsa Laban shekara 20. Yakubu ya fara yi wa Laban aiki na shekara 14 domin ya ba shi ’ya’yansa biyu ya aura, bayan haka, sai ya yi aiki na shekara 6 domin ya sami tumaki. (Farawa 30:25-33) Littafin nan Biblical Ar¯ chaeology Review ya ce: “Marubuta a zamanin da da kuma waanda suka karanta Littafi Mai Tsarki sun san da irin wannan yarjejeniyar, kamar wanda Yakubu da Laban suka yi.” ¯ Duwatsun da aka rubuta kwangila a zamanin da da aka tono a birnin Nuzi da Larsa da kuma wasu wurare a asar Irai sun nuna irin wannan yarjejeniyar. A irin wannan kwangilar, ana rarraba tumaki kowace shekara. Makiyaya suna karan rion tumaki kuma ana rubuta adadinsu da shekarunsu da kuma jinsinsu. Bayan shekara guda, mai tumakin yana karan ulu da madara da kindirmo da kuma ananan tumaki da dai sauransu. Duk arin da aka samu na makiyayin ne. aruwar da aka samu ya dangana ga adadin tunkiyar da aka ba makiyayin. Ana sa rai cewa tunkiya ari za su haifi ’ya’ya 80. Makiyayin zai biya idan wani tunkiya ko rago ya ace. Saboda haka, yana bukata ya kula da dabbar da yake kiwo. ˇ Yale Babylonian Collection SATUMBA–OKTOBA 2015 15 AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI Shin yadda rayuwar nan za ta kasance ke nan? Ka taa yin tunani cewa ma’anar rayuwa kawai ita ce yin wasa da aiki da aure da samun yara da kuma tsufa? (Ayuba 14:1, 2) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane masu hikima ma sun yi irin wannan tunanin.—Karanta Mai-Wa’azi 2:11. Shin rayuwa tana da ma’ana kuwa? Ya kamata mu fara yin wannan tambayar, Yaya rayuwa ta soma? Yadda Allah ya halicci wawalwarmu da kuma jikinmu ya sa mutane da yawa sun gaskata cewa akwai Mahalicci mai hikima. (Karanta Zabura 139:14.) Idan haka ne, yana da manufa mai kyau na halittar mu. Sanin wannan manufar za ta taimaka mana mu yi rayuwa mai ma’ana. KANA GANI MUNA CIKA SAURIN MUTUWA NE? Don arin bayani, ka duba babi na 3 a wannan littafin, Shaidun Jehobah ne suka wallafa Me ya sa aka halicci mutum? Allah ya albarkaci iyayenmu na farko kuma ya ba su aiki mai kyau. Manufarsa ita ce su cika duniya da ’ya’ya, su sa ta zama aljanna kuma su rayu har abada a cikinta.—Karanta Farawa 1:28, 31. An jinkirta manufar Allah sa’ad da iyayenmu suka taka dokarsa. Amma Allah bai fid da rai a kanmu ba kuma bai canja manufarsa ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah yana kan aiki tuuru don ya ceci mutane masu aminci kuma ya aiwatar da manufarsa ga duniya. Saboda haka, Allah yana so ka ji dain rayuwa yadda ya nufa tun asali! (Karanta Zabura 37:29.) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai sa ka koyi yadda za ka amfana daga nufin Allah. Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha MENENE Ainihi LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA? Don Allah ku turo mini littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? YARE SUNA ADIRESHI Idan kana neman adireshinmu, ka duba shafi na 2 Ka sauko da wannan mujallar da na kwanan baya kyauta p Akwai Littafi Mai Tsarki a harsuna sama da 100 a Intane Ka shiga dandalin www.jw.org/ha kai tsaye ko ka yi scan in wannan alamar da na’urarka wp15 09/01-HA 150603 s n o ZA KA SAMI AMSOSHI GA ARIN TAMBAYOYI GAME DA LITTAFI MAI TSARKI A INTANE